Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Za Ta Fara Kwashe 'Yan Kasarta Daga Nijar 


'Yan kasar Faransa da ke ficewa daga Nijar
'Yan kasar Faransa da ke ficewa daga Nijar

 Faransa ta fada a jiya Talata cewa za ta fara aikin kwashe ‘yan kasarta da sauran ‘yan kasashen Turai daga Nijar biyo bayan kusan mako guda da gwamnatin mulkin soja ta kwace mulki.  

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an dauki matakin aiwatar da kwashe mutanen ne sakamakon auna ofishin jakadancin Faransa a Yamai a wani tashin hankalin da aka yi da kuma rufe sararin saman Nijar. Ma'aikatar ta ce 'yan kasar Faransa sun gaza barin kasar da kansu.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron

A jiya Talata, Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya fada a shafukan sada zumunta cewa, Italiya ma tana baiwa 'yan kasarta da ke birnin Yamai wani jirgin na musamman na ficewa kasar.

Antonio Tajani
Antonio Tajani

Itama Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu Amurka na nazarin halin da ake ciki kafin ta yanke shawara ta karshe game da ko za ta janye tallafin soji daga Nijar, babbar kawarta ta yaki da ta'addanci a yankin.

"Fatanmu, da kuma abin da muke aiki akai, shine sojoji za su sauka, su baiwa shugaba Mohamed Bazoum damar ci gaba da mulkinsa," Linda Thomas-Greenfield tana fadawa manema labarai.

Linda Thomas-Greenfield
Linda Thomas-Greenfield

Jakadan Nijar a Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri ya shaidawa Muryar Amurka a ranar Talata cewa, “Shugaba Bazoum na cikin koshin lafiya. Kamar kowane dan Nijar a ketare, ina bibiyar lamarin cikin bakin ciki.”

Mamadou Kiari Liman-Tinguiri - Jakadan Nijar Ta Kasar Amurka
Mamadou Kiari Liman-Tinguiri - Jakadan Nijar Ta Kasar Amurka

A ranar 26 ga watan Yuli ne shugabannin sojoji suka yiwa Bazoum daurin talala tare da bayyana Janar Abdourahamane Tchiani, kwamandan masu tsaron fadar shugaban kasa a matsayin sabon shugabansu a ranar Litinin. Jagororin juyin mulkin sun ce sun yin hakan ne a matsayin martani ga abin da suka bayyana a matsayin matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa da kuma gazawar gwamnati wurin daukar kwararan matakan yaki da masu ikirarin jihadi.

Kungiyar ECOWAS ta kakabawa shugabannin juyin mulkin takunkumi tare da sanya wa'adin mako guda a ranar Lahadi don dawowar Bazoum a kan mulki. In ba haka ba, za ta yi amfani da karfin tsiya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG