Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Faransa Da Kai Hari Kan Sojojin Nijar A Jihar Tilabery - Amma Ta Karyata


Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun zargi kasar Faransa ta kai hari kan wasu askarawan kasar da sanyin safiyar yau Laraba 9 ga watan Agusta a wani kauyen Jihar Tilabery, abin da ya haddasa asarar rayuka, koda yake kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.

NIAMEY, NIGER - Lamarin ya faru ne a wajejen karfe 6:30 na safe a kauyen Bourkou Bourkou dake km 30 da mahakar zinaren garin Samira na jihar Tilabery inda wani jirgin sojan Faransa Samfarin A 400M da ya taso daga kasar Chadi ya afkawa dakarun tsaron Nijar a cewar sanarwar da Kakakin Majalissar sojoji ta CNSP kanal Amadou Abdourahamane ya karanta a kafar talbijan RTN mallakar gwamnati.

Jirgin wanda ya tashi da karfe 6:01 na safe ya keta matakin rufe sararin samaniyar da Nijar ta dauka a baya-bayan nan da nufin kare kanta daga barazanar harin da kasar ke fuskanta sanadiyar juyin mulkin na 26 ga watan Yulin 2023.

Kawo yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka rasu ba sakamakon faruwar wannan al’amari da ke gaskanta zargin da ake yi wa Faransa dangane da alakar da ke tsakaninta da kungiyoyin ta’addanci a cewar wannan sanarwa wacce ta kara da cewa wannan wani yunkuri ne da kasar Faransa ta sa gaba da nufin haddasa tashin hankali a Nijar, a ci gaba da neman hanyoyin bata sunan Majalisar soja ta CNSP a kuma shiga tsakaninta da al’ummar Nijar kamar yadda abin ya wakana a kasashen Mali da Burkina Faso.

To sai dai dazun nan hukumomin Faransa sun musamta zargin da sojojin Nijer suka yi akan cewa dakarun Faransa sun Kai farmaki kan sojojin Nijer a kauyen Bourkou Bourkoun jihar Tilabery a yau laraba 9 ga Watan Ogusta.

Haka Kuma hukumomin na Faransa sun wallafa wata takardar da ke nunin Hafsan hafsoshin Nijer ya ba jirgin sojojin su izinin ratsa Kasar Nijer domin gudanar da Wani Aikin da ke da nasaba da aiyukan rundunar sojojin Faransa da ke sansani a yammacin kasar.

📍Har yanzu muna bin diddigen wannan labarin don kawo muku cikakken rahoton agaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG