Sojojin sun binciki gidaje da mutanen dake wannan ruga a kauyen Unguwar Mangwaro dake karamar hukumar Sarkin Fawa
WASHINGTON, DC —
Rundunar sojojin Najeriya a Jihar Neja, ta ce dakarunta ne suka kai sumame a wata rugar Fulani dake kauyen Unguwar Mangwaro, a yankin karamar hukumar Sarkin fawa ta jihar.
Sojojin suka ce wannan wani bangare ne na kokarin da suke yi wajen kawar da duk wata matsakar da ake zaton akwai, koda yake mutanen wannan ruga sun ce hankulansu sun tashi matuka, kuma sojojin sun ci musu zarafi.
Kakakin Fulanin, Adamu Iliyasu Mugaure, yace su na sallar asuba ne sai suka ga sojoji cikin motoci 6 sun kewaye gidajensu, inda suka sanya kowa ya kwanta a kasa, babban da yaro, mace da namiji, suka shiga cikin dakunansu suka rika bude dukkan buhunan hatsi dake ciki.
Yace a bayan da suka gama binciken abubuwan da suka kai su can, sun kama wasu yaransu guda biyu suka tafi da su.
Malam Adamu Mugaure, yace sojoji sun kuma kwace dukkan wayoyinsu sun tafi da su.
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadarai tare da bayyana takaicin wannan ainda ta kira cin zarafin da sojoji suke yi ma al'ummarsu. Sakatren Miyetti Allah a jihar Neja, Muhammad Abubakar Sadiq, yace wannan al'amari ya tayar da hankulan mazauna wannan ruga, inda wasu suka gudu zuwa wasu garuruwa dake kusa a saboda fargaba.
Yace ya kamata a duk lokacin da jami'an tsaro zasu gudanar da wani aiki, to su yi shi cikin mutunci ba tre da firgita jama'a ko cin zarafinsu ba.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya a Minna, Jihar Neja, Kyaftin Salisu Mustapha, yace wannan sumame wani bangare ne na ci gaba da wani aiki na musamman na binciken wuraren da suke tsammanin za a iya samun matsala.
Yace mutanen da aka kama ana ci gaba da gudanar da bincike kansu, kuma za a sako su da zarar an kammala an ga ba su da laifin komai.
Wannan sumame yana zuwa ne kwanaki biyu rak a bayan wata ganawar da aka yi a tsakanin gwamnonin jihohin arewa da shugabannin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah domin samo hanyoyin magane irin matsalolin tsaron da suke addabar yankin.

Your browser doesn’t support HTML5