Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Sojoji Akan Fulani Ya Bani Tsoro - inji Sarkin Fulani


Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

Biyo bayan harin da aka ce sojoji ne suka kai akan Fulani a jihar Nassarawa, shugabannin Fulani sun fara mayar da martani.

Mutane da dama sunka rasa rayukansu a dalilin wani farmakin da sojoji suka kai wa rugagen Fulani a keana dake cikin jihar Nasarawa.

Kawo yanzu ba’a san dalilin da yasa sojojin suka kai wannan harin ba, ganin cewa kura ta lafa dagane da rashin jituwar da aka samu a kwanan baya a jihar.

Senata Walid Jibrin, wanda kuma shine sarkin Fulanin Nasarawa, yace abun ya bashi mamaki kuma ya bashi tsoro kwarai da gaske, masamman ganin yanda aka fara yunkuri na masamman da sarakuna Fulani keyi na zaman lafiya, kuma a cewarshi, hakika an fara samun nasara bisa ga wannan yunkuri.

Senata Jibrin ya kara da cewa gwamnatocin Nassarawa da Binuwe sun kafa babban kwamiti na sulhu tsakanin makiyaya da manoma, da kabilu wanda a Nassarawa aka nada Andoma wato sarkin Doma ya zama shine shugaba, kwatsam sai ga kuma wannan kashe-kashe wanda aka ce sojoji suka aikata.

Sanata Walid Jibrin, yace afkuwar wannan bai yi dadi ba, kuma yayi kira da ayi cikakken bicike kuma da hana faruwar irin wanna a gaba.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG