Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Hasarar Rayuka da Dukiyoyi a Yankin Takum


Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.
Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.

Maharan da suka kai farmaki kan Kashimbila dake karamar hukumar Takum, sun kuma yi gaba da wasu mata, tare da kona gidaje da masallatai.

Rahotanni daga yankin kudancin Jihar Taraba na cewa an kashe wasu mutanen da ba a san adadinsu ba, tare da raunata wasu, a sabon farmakin da aka kai kan Kashimbila dake yankin karamar hukumar Takum.

Mutanen da suka kubuta da rayukansu sun yi zargin cewa maharan sun kuma sace wasu mata sun tafi da su.

Wani mazaunin garin, ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa wannan fada ya samo asali ne daga rikicin Fulani makiyaya da Tiv, amma sai aka kawo farmaki a kan unguwannin Hausawa na Kashimbila, inda aka kona gidaje da masallatai, sannan aka saci wata matar aure da wata budurwa guda daya.

Mutumin yace wani yaro karami ya kone kurmus a cikin dakin da aka cinna ma wuta a garin.

Yace ya zuwa lokacin dai jami'an tsaro ba su isa wannan gari ba.

Rundunar 'yan sandan Jihar Taraba ta tabbatar da abkuwar wannan tashin hankalin, inda kakakinta ASP Joseph Koje yake fadin cewa an tura karin 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin domin suyi kokarin kashe wutar wannan fitina.

Yace su na binciken rahotannin cewa an sace wasu mata.

Gwamnatin jihar Taraba ta tura jami'anta da suka fito daga wannan yanki domin suyi kokarin kwantar da wutar tashin hankali.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG