Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na Jihar Neja, Alhaji Yusuf Garba Tagwai, shi ya jagoranci aikin kore Fulani makiyayan, inda yace a halin yanzu sun yi sansani a kauyen Gunu dake yankin karamar hukumar Shiroro.
Kwamishinan yace a bayan dal;ilai na tsaro, wadannan makiyaya sun mamaye gonaki ne na 'yan kabilar Gwari a inda suka yi sansanin. Yace hakan na iya barazana sosai a saboda su na iya yin barna ga kayan abinci, kamar doya, wadanda ake bari a cikin gonakin.
Amma kuma kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Neja ta yi watsi da wadannan hujjoji da hukumomin suka bayar, tana mai fadin cewa wadannan makiyayan ba wai baki ba ne, wadanda aka mamaye wa gidaje ne a yankin dake makwabtaka da Neja a Jihar Kaduna.
Shugaban Miyetti Allah a Jihar neja, Alhaji Sama'ila Rebe, yace wadannan makiyaya ba su da wata matsala, sanannu ne.
Shi ma babban darekta a ma'aikatar kula da harkokin makiyaya a ofishin gwamna, Alhaji Abubakar Sadiq, yace bai kamata a dauki irin wannan matakin ba, har sai an tuntubi shugabannin da gwamnati ta dora ma alhakin irin wannan lamarin, da shugabannin Fulani makiyayan.
Su ma makiyayan da aka ayyana korar da suka yi magana sun bayyana cewa dukkansu daga Kaduna suke, kuma kwace musu filaye yasa suka yi kaura.