Yanzu al'ummomin sun yi yarjejeniyar dakatar da fadace fadace tsakaninsu da rugumar zaman lafiya. Sun sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban kwamitin da gwamnatin tarayya ta nada karkashin shugabancin mataimakin sifeto janaral na 'yansanda Michael Zuokumor. Al'ummomin sun yadda zasu daina fada da juna.
Wani Peter Igbace shugaban matasan Tibabe na jihar Nasarawa yace al'ummarsa da ta Fulani sun zauna sun tattauna game da zaman lafiya. Yace amma yarjejeniyar ba zata tabbata ba sai sun shiga daji su fadakar da mutanesu. Yace idan Fulani sun yi rikici zasu kawosu gaban hukuma. Haka ma su Tibabe idan dayansu ya yi rigima zasu kawo shi gaban hukuma.
Shi ma Alhaji Muhammed Usaini sakataren Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa yace daga yau babu sauran rikici tsakaninsu da Tibabe. Zasu kafa kwamiti a kowace karamar hukuma su tunkari duk bata garin dake bata masu daji. Tibabe su koma inda suke. Fulani ma su koma inda suke su yi kiwo kana gwamnati ta taimaka domin sun gaji da rikici. Yace rikicin ya hanasu cigaba. Yunwa ta damu mutane a yankunan Nasarawa da Binuwai
Barrister C. T. Chahu daga Kadarko a jihar Nasarawa yace sun yi yarjejeniya da 'yanuwansu Fulani. Wadanda suke gudun hijira su dawo. Kuma sun yadda kada a sake samun rikici a kauyukansu. Hakama Haruna Garba Golo yace zasu zauna da dattawansu da matasansu su fahimtar da su domin sun yadda su yi zaman lafiya.
Mataimakin Sifeto Janaral yace manufar kwamitin ita ce su lalubo zaren sasantawa da makiyaya da manoma. Bukata ta biya domin al'ummomin biyu sun yadda su zauna lafiya da juma su kuma hada kai da jami'an tsaro wurin gano masu tada karin baya.
Ga rahoton Zainab Babaji.