Dr. Ephraim Goje shugaban kungiyar 'yan kudancin Kaduna ko SOKAPU shi ya jagorancin nashi bangaren suka zauna da shugabannin Fulani domin cimma yarjejeniyar. Inji Dr Goje zaman nasu na jiya shi ne karon farko da suka taba zaunawa tare su tattauna matsalolin dake kawo rashin zama lafiya. Yace a yi hakuri da juna. A yafewa juna domin a samu dawamammen zaman lafiya.
Bangarorin biyu sun kafa kwamiti na mutum tara domin kulawa da abubuwa da suka damesu kafin a kaiga kashe-kashen juna. Kwamitin zai dinga yin taron fahimtar juna daga lokaci zuwa lokaci.
Shi ma shugaban kungiyar Fulani Miyetti Allah ta jihar Kaduna Ardo Ahmadu Suleiman ya sanya hannu a madadin Fulanin kudancin Kaduna. Yace abun da aka cimma abun farin ciki ne da murna. Duk mutumin dake duniya babu abun da yake bukata irin zaman lafiya. Yace sun zauna kuma sun yadda a zauna lafiya. Duk mutanen dake kawo masu tashin hankali su tonasu kuma Allah ya tona masu asiri. Ya kira gwamnati ta sa ido kan kare dukiya da lafiyar al'umma.
Kwamishanan 'yansandan jihar Kaduna Umar Usman a bagansa aka sanya wa yarjejeniyar hannu. Yace wannan abun da aka yi alama ce an samu zaman lafiya tsakanin Fulani da sauran al'ummar kudancin Kaduna. Yace dama kowa ya gaji da abun dake faruwa.
To saidai a lokacin taron kulla yarjejeniyar wasu kungiyoyi daga kudancin Kaduna sun yi taro inda suka yi korafin su basu ga wani dalilin kulla yarjejeniya ba. Barrister Zakariya Zoffa ya yi jawabi a madadin kungiyoyin yace an dade ana irin wannan zancen amma ana zuwa ana kashe mutanensu. Yace sun yi magana, sun rubuta sun yi kuka kuma gwamnati ta gani amma babu abun da aka yi a tabbatar ba zai sake faruwa ba. Yace yarjejeniyar a kan menene domin su basu yi masu wani abu ba.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.