Shugaba Buhari ya kama hanyar cika alkawuran da ya yi

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shaikh Yakubu Musa Hassan Katsina yace masu cewa har yanzu gwamnatin Buhari bata samu nasara akan abubuwan da ta sa gaba ba su tambayi al'ummar jihohin arewa maso gabas kamar Yobe da Borno inda yanzu suna barci ba tare da shakku ba, yara na zuwa makarantu ana shiga masallatai da asubahi da kuma zuwa mijami'u lami lafiya.

Idan 'yan arewa ne suke fadan hakan mazauna Abuja ne domin basu san abun da jihohin Borno, Yobe da sauransu suke ciki ba kafin Buhari ya karbi madafun ikon Najeriya.

Bala'in da ya addabi arewa maso gabas har ya isa Kano, Kaduna Abuja da wasu garuruwan arewa kafin zuwan Buhari. Kashe kashe sun hana mutane zuwa wurin ibada a jihohin arewa maso gabas. Yau lamarin ya canza. A jihohin Borno,Yobe, da Adamawa mutane sun soma samun walwala.

Yanzu kamata ya yi 'yan siyasa masu gwamnati da na adawa su bar makamansu su hada hannu da gwamnati a shawo kan bala'i na fatara da yunwa da suka addabi kasar. Su zo a yi gyara dasu amma ba su rike kasafin kudi ba.

Dangane da alkawuran da shugaba Buhari ya yiwa kasa, Shaikh Yakubu Musa Hassan Katsina yace shugaban ya dauki hanyar cikasu. Tushen cikasu shi ne a samu zaman lafiya. Na biyu a datse satar dukiya da mutane ke yi abun da shugaban yake yaki dashi yanzu. Idan an baiwa shugaban kasa hadin kai nan da shekara daya ko biyu zai dawowa Najeriya martabarta.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari ya kama hanyar cika alkawuran da ya yi- Sahaikh Hassan Katsina - 3' 30"