Wannan amincewar dai ta biyo bayan tattaunawar da akayi a wani taro na Majalisar Tattalin Arziki ta gwamnatin Tarayyar Najeriya. wadda ta kunshi wasu gwamnoni da wasu Ministoci masu baiwa gwamnati shawara kan tattalin arziki.
Bayan da aka kammala taron ne gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura, yayiwa manema labarai karin bayani dangane da matsayar da aka cimma a wurin taron, inda yace matsalar lalacewar tattalin arzikin da ta samo asali daga gwamnatin da ta gabata itace ta jefa jihohi cikin matsalar rashin biyan ma’aikatansu albashi.
Taron dai ya kunshi wasu jami’an ma’ikatun gwamnati da dama wanda sukayi bayanin kan yadda ake kokarin shawo kan duk matsalolin dake haddasa tsaiko ga tattalin arzikin kasa dama abubuwan ciyar da rayuwa gaba a kasar, kamar wutar lantarki da Man fetur.