Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Yanzu Da Na Baya Akwai Banbanci


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari ya bukaci goyon bayan Bankin duniya da dauran kasashe

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da mukarrabansa a yau sun karbi bakuncin Ms. Mulyani Indrawati, babbar darakatan gudanawar ta Bankin duniya tare da kusoshin Bankin domin yin nazari akan hanyoyin da Bankin zai bi domin tallafawa Najeriya, domin fuskantar kalubalen dake gaban ta na batun tattalin arziki da tsaro da sauran harkokin yau da kullum.

Bayan da aka kammala ganawar ne Ms. Indrawati, ta bayyanawa manema labarai ciki harda wakilin muryar Amurka, tana cewa ganawa da shugaba Buhari, yana da mahimmancin gaske a daidai lokacin da Najeriya, ke fuskantar kalubale daban daban.

Tace wannan muhimmiyar dama ce da suka yi amfani da ita domin tattaunawa da fahimtar kalubale da matsaloli na tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta kamar yadda sauran kasashen duniya ke fama, dangane da tabarbarewar tattalin arziki a duniya baki daya da faduwar darajan mai.

Ta kara da cewa dalilin da yasa kennan wakilan Banki duniya suka zauna da shugaban Najeriya, da sauran wakilan Gwamnati domin duba hanyoyin da Bankin duniya zai bi domin bada tallafi domin Najeriya, ta fito daga kangin da take ciki a yanzu in ji babbar daraktar gudanarwa ta Bankin duniya.

Shugaba Muhammadu Buhari, yace Najeriya, na fatar samun gudumawa da goyon baya na wannan Banki da duk kasashen da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an dawowa Najeriya, da kudadenta da aka sace aka ajiye a kasashen ketare masamman a Switzerland.

Inda aka bada misali da kudaden da aka samu na janar Sani Abacha, da kasar Switzerland, ta rike tana cewar bazata baiwa Najeriya kudaden kai tsaye ba sai dai a bada ta Bankin duniya domin a yiwa kasar Najeriya aiki ganin irin matsalolin da aka fuskata a baya cewa ana turo irin wadannan kudaden amma ana batar dasu ta hanyar da ba ‘yan Najeriya, ke cin moriya ba inda Muhammadu Buhari ke cewa yanzu da can baya akwai banbanci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG