Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisun Najeriya zasu kammala gyaran kasafin kudi wannan makon - Danjuma Goje


Sanata Muhammadu Danjuma Goje
Sanata Muhammadu Danjuma Goje

Sanata Danjuma Goje ya fadawa Muryar Amurka cewa kai-komo da kacenace da ake yi akan kasafin kudin kasar na wannan shekara ya kamata ya tsaya haka a hanzarta a yi gyaran da shugaban kasa yake so domin ya kama iaki gadan gadan.

'Yan majalisar dattawa da na wakilai dole ne su hada kai, su daidaitu domin su aiwatar da duk gyare-gyaren da ake bukata a yi a mayarwa shugaban kasa ya sa hannu ya cigaba da aiki.

Sanata Danjuma Goje yace a cikin wannan satin da aka shiga zasu kammala gyare-gyaren saboda duk alamuran kasar da al'ummarta sun dogara ne ga kasafin kudin. Yace yanzu komi ya tsaya saboda haka ba zasu cigaba da siyasa ba. Dalili ke nan suka kira majalisar wakilai su hada kai su yi gyaran da shugaban kasa ke bukata cikin wannan satin.

Sanata Danjuma Goje ya ki ya yi magana akan zargin cewa kwamiti dinsa ne ya hana ruwa gudu. Yace kokarin da suke yi yanzu shi ne na kashe wutar da ta taso, wato a gama da batun kasafin kudi a cigaba da aiki domin jama'a su samu sauki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG