Kakakin rundunnar sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka yace babu shakka shugabannin sojoji da duk jamai'an tsaro suna warware duk wani kulle-kullen 'yan ta'adan.
Yace 'yan Boko Haram sun fito da wasu sabbin salo yadda zasu cigaba da addabar jama'a. Sabbin salon sun hada da sanya kayan sarki irin na sojojin Najeriya amma suna daura igiya a wuya da kafa. An fadakar da jama'a domin suna sake kamanni su shiga wurare da dama saboda hare-haren da suke samu ta sama da kasa daga dakarun Najeriya.
Wasu da basu sani ba suna daukansu tamkar 'yan agaji ko wasu jami'an tsaro ne har su samu su yi barna..
Wani zibin kuma sukan nuna cewa su wadanda aka ceto ne ko kuma suka gudo daga sansanin 'yan ta'adan na Sambisa. Idan sun shiga cikin jama'a sai su dinga barna.
Kukasheka yace yaki da ta'adanci abu ne da jama'a zasu hada karfi da karfe ba na sojoji kadai ba ne. Sojoji na iyakar bakin kokarinsu amma jama'a sai sun yi la'akari cewa dole ne su marawa sojoji baya kafin a kaiga nasara.
Wani salon shi ne na gurbata ruwan sha tare da dasa nakiyoyi a gonaki.
Ga karin bayani.