Manufar taron shi ne domin duba koke-kokensu da irin matsalolin da suka fuskanta da kuma sanin matakan da suka kamata a dauka saboda kawowa jihohin saukin halin da suka samu kansu ciki
Tun lokacin da aka karbi mulki daga gwamnatin PDP jihohin suka samu kansu a wani mawuyacin hali na rashin kudi.
Kamar yadda gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudo ya bayyana yace lallai gwamnoni sun gamsu cewa shugaban kasa ya basu karfin gwiwar cewa za'a bi ka'idodi wajen kashe kudin gwamnati ta yadda za'a share hawayen 'yan kasa saboda fatara da lalacin da aka fuskanta a mulkin kasar.
Yace shugaban ya tabbatar a karkashin jagorancinsa abubuwa zasu gyaru ba kamar yadda suke da ba. Kowa ya ji karfi kuma gwamnonin zasu je su aiwatar da abubuwan da suka koya daga shugaban a jihohinsu. Misali jihar Kebbi na iya noma shinkafar da zata ciyar da kasar gaba daya ba sai ta shigo da ita ba lamarin da zai taimaki jihar da kudin shiga.
Shi ma Alhaji Abubakar Badaru na Jihar Jigawa yace ko shakka babu sun gamsu. Su a Jigawa sun rage kudin kashewa a ma'aikatun gwamnati da kusankasi hamsin. Sun gayyato Aliko Dangote akan yadda za'a samu masana'antun shinkafa da sukari.
Ga cikakken bayani daga Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5