Rahotanni daga Amurka na cewa kasar na shirin tura dakarunta zuwa Najeriya domin agazawa sabon shugaban kasar Muhammadu Buhari da dakaru wajen inganta tattara bayanan sirri da tsare-tsare.
A yau Juma’a wannan sanarwa ta fito daga ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka.
A baya, matsalolin da suka dabaibaiye dangantaka tsakanin masu ba da shawara a bangaren dakarun Amurka da na Najeriya kan take hakkokin bil adama da cin hanci da rashawa, sun kasance babban shinge ga kokarin da ake yi na kawo karshen hare-haren Boko Haram da aka kwashe shekaru shida ana fama da su.
Sanarwa ta kara da cewa shugaba Buhari za su tattauna da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, kan yadda za a shawo kan wannan matsala da kuma yadda kasashen biyu za su fadada huldar kasuwanci anan gaba.
Bangarori biyu za su tattauna ne a gefen taron rantsar da sabuwar gwamnatin Buhari wanda aka gudanar a yau Juma’a a Abuja, babban birnin kasar.
Kerry shi ke jagorantar tawagar kasar Amurka a wannan bikin rantsar da gwamnatin ta Buhari.
Wata majiya kwakkwara ta bayyana cewa tattaunawar farko da aka yi kafin zuwan Kerry Najeriya, ta nuna alamun cewa Buhari na son ya yi dangantaka ta kut da kut da Amurka.
Kamfanonin Amurka da dama na son saka jarinsu a fannin mai fetur da iskar gas da kuma fannin kere-kere.