Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Tayi Watsi da Kasafin Kudin Bana


Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) Abdulwaheed Omar
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) Abdulwaheed Omar

Kasafin kudin da gwamnati mai shudewa ta gabatar da kuma majalisun kasar suka amince dashi bai tabo batun tallafin da aka saba baiwa man fetur ba

Kungiyar kwadago tayi watsi da kasafin kudin na Najeriya ne domin ya cire tallafin man fetur gaba daya.

Kungiyar tana ganin gadar zabe aka yiwa gwamnatin da zata karbi mulki. Kungiyar tace sabuwar gwamnatin zata samu matsala da 'yan kasar da ma ita kanta kungiyar kwadago.

Kasafin kudin da ya dara nera tiriliyan hudu an ginashi ne akan sayar da gangar mai a kasuwar duniya dalar Amurka hamsin da uku. Kananan ayyuka na da kashi tamanin cikin dari manyan ayyuka kuma nada kashi ashirin.Amma babu ko kwandala akan tallafin albarkatun man fetur. Wannan abun ne kungiyar kwadago tace ba zata amince dashi ba.

Nasiru Kabir wani jami'in kungiyar kwadago yace abubuwan da aka bayyana akan kasafin kudin sun nuna akwai wata manakisa da basu fahimta ba . Yace gwamnati mai ci yanzu ta fito ta yiwa mutane bayani dalla dalla ta fitar da mutane daga cikin zargin da ake yi mata. Yace sun lura gwamnati tayi ne saboda gwamnati mai shigowa ta samu mummunan wahala da 'yan Najeriya.

To amma sakataren dillalen man fetur na kasa Danladi Fasali yace cire tallafin shi ne zai kawo karshen wahalar da 'yan kasar ke sha akan rashin man fetur din. Yace shi tallafin baya taimakawa talakan Najeriya. Yayi misali da batun kananzi da aka kashe biliyoyin nera a kansa amma kuma babu shi. Yace NNPC ce ke sayar da kayanta tana yaudarar mutane. Har yau dan Najeriya na sayen kananzir da tsada

Wani kwararre a harkokin tattalin arziki Abubakar Ali yace kasafin kudin nada matsaloli da yawa. Yace dole idan sabuwar gwamnati ta kama mulki ta cire wasu abubuwa, tayi gyaran fuska. Gwamnatin dake neman canji ba zata iya yin anfani da kasafin ba. Duk wasu gyare-gyare da sabon shugaban kasa yayi sai ya mikawa majalisun tarayya su duba.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG