Sabbin hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaiwa Maiduguri ya dauki hankalin mutane lamarin da ya sa ana ganin dalilin da ya sa shugaban kasa ya gana da hafsoshin kasar da kuma shirin kai ziyara kasashen Nijar da Chadi. Taron na iya zama na duba hanyoyin da kasar zata tunkari kungiyar Boko Haram a gama dasu gaba daya.
Amma masana tsaro irinsu Manjo Yahaya Shinku na ganin zai yi wuya su hafsoshin su dore akan kujerunsu a karkashin shugabancin Muhammad Buhari. Su hafsoshin aka baiwa alhakin yakar Boko Haram a gwamnatin da ta shude. Da sabuwar gwamnati maimakon su cigaba da aikin da aka basu zasu bata lokaci ne suna kokarin rufawa kansu asiri kada a gane kurakuransu da barnar da suka yi. Tana yiwuwa ma su dinga yin abun biyan bukatun kansu maimakon su taimakawa sabon shugaban kasa.
Dangane da cewa sojoji babu ruwansu da siyasa aikinsu suke yi Shinku yace a da ke nan. Yanzu har kama kafa suke yi na neman mukami.Yace wasu ma basu cancanta a basu mukaman ba amma ake basu. An kori wadanda suka fisu kwarewa kana aka basu mukamai. Yace dole a fadi gaskiya domin sabuwar gwamnati mai son ta zabi wadanda suka cancanta ne ta basu mukami.
Usman Usman na kungiyar Fulani yace duk wani garanbawul da za'a yiwa harkokin tsaro zai yi tasiri ne idan ya shafi sashen 'yansanda domin akwai yawan baragurbi a cikinsu.
Ga karin bayani daga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.