Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Goyon Bayan Matakin Buhari – inji Kasashen Makwabta


[FILE PHOTO]
[FILE PHOTO]

Kasashen dake Makwabtaka da Najeriya, kama daga Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru suna nuna goyon bayansu game da muhimmancin yaki da Boko Haram.

Tuni sabon shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a mayar da cibiyar rundunar sojin kasar yaki da Boko Haram Maiduguri.

Sabon harin Bom a Maiduguri ya kara nuna muhimmancin yaki da masu tayar da kayar baya, da kan aukawa talakawa wadanda basu da laifin komai, sai ma rasa rayuka da suke yi da dukiya da dama.

Janar Saleh Maina mai ritaya wanda rundunar shi ta kama tsohon shugaban Boko Haram Muhammadu Yusuf, yayi farin ciki da sabon matakin, da dama yake gani sakaci ne ya ta’azzara matsalar.

“Tun daga farko ya kamata da anyi maganin wannan abun. Kuma an dan kokari, sai dai akwai rashin gaskiya da yawa a ciki”, a cewar Janar Maina.

A nasu bangaren, kasashen makwabtan Najeriya dake fama da wannan matsala na nuna karin goyon baya ga yakin.

Baya ga Shugaba Idris Deby na Chadi da ya nanata bada goyon bayan, dan majalisar dokokin Nijar Sani Bukar yace kasar sa bata da zabi ga wannan yakin.

Masu sharhi na fatan gani sabuwar gwamnatin ta mayar da hankali kan batutuwan tsaro, kafin dawo da hankali kan sauran batutuwa.

Muna Goyon Bayan Matakin Buhari – inji Kasashen Makwabta – 3’30”
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG