An yi tarukan addu'o'i na cigaban Najeriya da samun zaman lafiya a birnin Legas wadanda 'yan Najeriya da dama suka halarta.
Tarukan sun biyo bayan kiran da sabon shugaban kasar Muhammad Buhari yayi cewa a yi addu'ar samun zaman lafiya tare da goyon bayan gwamnatin tarayya.Ya nemi addu'ar samun magance dimbin matsalolin da suka addabi kasar.
Wasu da suka halarci taron addu'o'in sun ce sun yi hakan ne domin sabon shugaban ya gaji matsaloli iri-iri kuma yana bukatar addu'a saboda ya samu ya shawo kansu.
Yayin da ake yin addu'o'in wani jigo a jam'iyyar APC Architect Kabiru Ahmed yace dole sai jama'a sun nuna jimriya da goyon baya ga sabuwar gwamnati shi ne shugaban kasar da mataimakinsa da sauran mukaarraban gwamnati zasu samu su ciwo kan matsalolin dake ciwa Najeriya tuwo a kwarya. Yace addu'a ce ta kawosu inda suke yau. Saboda haka a cigaba da yiwa kasar addu'a da shugabanninta.
Ga rahoton Babangida Jibril.