Wani muhimmin batu da ya taso shi ne na kudade da aka ce za'a baiwa 'yan majalisun da zasu yi anfani dasu wajen sayen kayansu na sawa.
An ruwaito cewa majalisun zasu raba kudi har nera biliyan casa'in. To amma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yace labarin shati fadi ne kawai. Yace kudin da ake basu kowane wata saboda sayen kayan sawa shi ne dubu arba'in da biyu. Yace idan an yi lissafi rigar da suke sawa tafi dubu hamsin. Mutane basu san menene abun ba. Yace kudin na 'yan majalisun biyu ne tare da ma'aikatansu.
Akan zaben sauran shugabannin majalisar dattawa Sanata Gaya yace zasu tattauna yau tsakanin su 'yan APC domin su gyara irin gurbin da aka samu kada a sake samun wake cikinsu kamar yadda ya faru a zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa. Yace bai kamata a ce irin hakan ya faru ba.
Dangane da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari zai mika wa majalisar dattawa sunayen ministoci Sanata Gaya yace su a majalisa suna cikin rikici saboda haka babu yadda shugaban kasa zai mika masu sunayen ministoci sai sun daidaita rikicinsu.
Yace 'yan Najeriya su sani cewa shugaba Muhammad Buhari a shirye yake ya gyara kasar gwargwadon iyawarsa. Kuma babu shakka zai rufe idonsa ya yi aiki.
A bangaren majalisar wakilai Hamisu Ahmed Mailantarki yace a nan ma basu kammala zaben shuwagabanni ba. Yace akwai kujeru na jam'iyya amma dole a samu hadin kai tsakanin jam'iyyar da shugabannin majalisa. Yanzu ana tattaunawa bayan hakan zasu fito da matsaya da zata biya bukatun kowa.
Ga rahoton Medina Dauda.