Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umurni ga hukumar dake binciken cin hanci da rashawa ta EFCC ta gudanar da cikakken bincike akan tsohon hafsan hafsoshin soji da tsohon hafsan sojin sama da wasu manyan sojoji su 17 tare da tsohon mai ba tsohon shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki akan zargin wata sabuwar badakalar,
Wannan sabuwar badakalar da ajka bankado ta faru ne a faggen sayo makamai da jiragen sama da sauran wasu ayyukan tsaro da suka wakana tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015.
Yanzu an gano cewa anakashe nera miliyan dubu ashirin da tara da dalar Amurka miliyan dubu biyu wurin sayo kayan yaki ma sojojin sama kawai kafin ma a je manya manyan bangarorin sojojin Najeriya kamar yadda bincike ya bayyana.
Banda hafsoshin sojojin masu aiki da wadanda suka yi titaya da za'a bincika akwai wasu kamfanoni guda ashirin da daya wadanda za'a gudanar da bincike a kansu domin dasu aka yi anfani wurin gudanar da badakalar. Ana ma kyautata zaton kamfanonin na wasu da ake zargin ne.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5