Farfasa Attahiru Jega shi ne shugaban farko tun lokacin Shugaba Ibrahim Babangida a tarihin hukumar da ya cika wa'adinsa ba tare da an tsigeshi ko kuma an tilasta masa ya yi murabus ba. Shi ne kuma shugaban da ya taba shirya zabuka har biyu a tarihin hukumar.
Farfasa Jega ya shirya zaben shekara ta 2011 kana ya shirta ta shekarar 2015. Duk zabukan duniya ta yaba da yadda aka gudanar dasu da kuma sakamakonsu.
Biyo bayan barinsa hukumar zabe jiya mutane sun soma furta ra'ayoyinsu game dashi. Wani Jibrin daga Gidan Dala dan jam'iyyar PDP yace da farko an yi anfani da Farfasa Jega ko kuma an yi anfani da mutanensa a zaben 2011. Ya bada misalin abun da ya faru a jihar Ogun. Wai kafin a kammala zaben wannan shekarar INEC ta bada sakamakon zaben. Amma ya gyara aikinsa inda ya fito da wani tsarin da ya inganta sakamakon zabe. Idan ya koma gida sai a yi masa godiya da fatan alheri.
Malami a jami'ar Abuja a fannin kimiyar siyasa yace abun farin ciki ne Farfasa Jega ya kamma wa'adin shekaru biyar a hukumar zabe ta INEC. Yace a matsayinsa na shugaban INEC yayi rawar gani. Yace a tarihi shi ne kadai ya yi zabe sau biyu shi ne kuma ba'a cireshi ba. Yakamata al'ummar Najeriya su yabeshi domin sabbin hanyoyi da ya kawowa hukumar zabe. Ya kara darajar zabe da kimansa.Ya jawowa Najeriya daraja a idanun duniya.
Sani Tahir dan jarida dake Abuja yace hakikan Farfasa Jega ya ci nasara. Yace zaben 2011 ya kawo masa kalubale saboda korafe korafen da suka biyo bayan zaben da rigingimun kashe-kashe da kone kone. Lamarin ya sa ya kuduri aniyar shirya zabe na gaba wanda ba'a taba yin irinsa ba a kasar. An yi zaben wanda yanzu ya shiga tarihin Najeriya. Ya yi kokari ya kwato wa talaka 'yancinsa na zaben abun da suke so ba a yi masu dauki dora ba. Yayi zaben 2015 ba domin ya muzgunawa Jonathan ko kuma ya farantawa Buhari rai ba. Yayi zabe ne domin ya bar tarihi ya kafa tushe mai tasiri da kuma kara karfin dimokradiya a Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5