Bayan shigar da kararraki da wasu jam'iyun Najeriya su ka yi na neman a kara wa'adin zabe, har ila yau wasu jami'yu a daya bangaren sun ce ba za su amince da hakan ba.
Shugaban jam'iyyar Labor, Alhaji Abdulkadiri Abdulsalami, ya ce babu adalci a wannan sabon yunkurin da wasu jam'iyyu da 'yan siyasa ke yi.
Ya ce idan aka sake dage zabe ba a yi wa mutanen kasar adalci ba ya na mai cewa sun amince da dagewar farko amma a wannan karon hakan ba za ta sabu ba tunda hukumar zabe ta ce a shirye ta ke.
"A lokacin da shugaban hukumar zabe Farfasa Jega ya kirawo shugabannin jam'iyyu bisa ga wasu dalilan dagewar da aka yi ta dace, amma ba yanzu ba." in ji Abdulsalami.
Dangane da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram, Abdulsalami ya ce abubuwa sun canza domin ana samun nasara akan su fiye da da.
Bugu da kari shugaban Chadi ya fito ya ce sun san inda shugaban Boko Haram yake kuma za su kamashi idan bai mika kai ba.
Akan raba katunan zabe, Shugaban jam'iayr ta Labor ya ce an samu ci gaba sosai domin shugaban hukumar zaben ya fada sun raba katuna da dama.
Kana game da ko sojoji za su sake fitowa su ce basu shirya ba Abdulsalami ya ce kada ma a yi irin wannan tunanin.
Ga karin bayani a rahoton Umar Faruk Musa.