Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Kotu Za ta Yanke Hukunci Kan Na'urar Zabe


Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega
Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega

Ana jiran babbar kotun tarayyar Najeriya ta yanke hukunci akan yin amfani da naurar tantance masu kada kuri'a a zabe mai zuwa

Babbar kotun tarayya za ta yanke hukunci yin amfani da na'urar tantace masu jefa kuri'a ko kuma jingine yin amfani da ita a wannan makon. Yanzu dai zaben saura kwana goma 12 a fara.

Kalubalen zaben na kawo bangaranci a Najeriya inda Farfesa Ango Abdullahi na kungiyar dattawan arewa ya ke amincewa da yin amfani da na'urar da kuma gudanar da zaben a karkashin shugabancin Farfasa Attahiru Jega.

To amma a can kudu maso gabas 'yan rajin kafa kasar Biafra sun yi gangamin a sallami Farfesa Jegan ma daga mukaminsa domin wai, ba zai yi adalci a zaben ba.

Su kuma 'yan PDP suna cewa kada a shafa masu kin jinin naurar. Sun kuma nuna cewa ko da menene za'a yi amfani da shi za su lashe zaben. Kakakin jam'iyyar Oliseh Metuh ya ce sun ma kama hanyar lashe zaben.

Wasu 'yan PDP sun ce a shirye suke su lashe zaben da cewa ita na'urar ba ta basu tsoro.

XS
SM
MD
LG