Duk da tabbacin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayar cewa ya gamsu da ayyukan shugaban hukumar zabe Farfessa Attahiru Jega, kuma bashi da wata niyyar cireshi daga kan mukaminsa, rahotanni a kafofin yada labaran Najeriya suna nuni da cewa ana cukucukun tura Farfessa Jega zuwa hutun dole.
Wakilin Sashen Hausa Umar Farouk Musa, ya tattauna da masanin shari'a Farfessa Awwal Yadudu na jami'ar Bayero ta kano, wanda yace tsarin mulki ne ya kafa hukumar kuma ta kayyade wa'adin kwamishinonin hukumar shekaru biyar.
Farfessa Yadudu, yace tsarin mulkin Najeriya ya kare martabarsu ta yadda babu wani jami'in gwamnati kama daga shugaban kasa zuwa kasa, wanda zai tilasta musu yi ko hana su daukan wani mataki da a ganinsu ya dace ba.
Da aka tambayeshi ko abunda ya faru da tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi, yana iya faruwa da shugaban hukumar zabe? Farfessa Yadudu ya ce a'a, saboda tsarin mulki ya yi tanadi na wa'adin aikinsa, babu damar a rage masa.
Farfessa Yadudu yace an sami irin haka a jihar kwara inda Gwamnan jihar ya sauke shugabannin hukumar kamin wa'adin aikinsu ya kare, shari'ar ta je har a gaban kotun koli, ta yanke hukuncin cewa ba dai dai bane matakin da Gwamnan jihar ya dauka.
Ga karin bayani.