Fitar da sunayen ‘yan takarar Shugaban kasa 14 da hukumar zabe ta yi, ga masu kada kuri’a miliyan 68 na nuna kankamar shirin zaben, wanda ake ganin hakan ya rage fargabar dagewa koma rashin gudanar da zaben a ranar 14 ga watan gobe.
Wakilinmu a Abuja wanda ya aiko ma na da wannan rahoton Nasiru Adamu Elhikaya, ya ruwaito shugaban hukumjar zabe Furfesa Attahiru Jega na zayyana sabbin dabarun hana magudin da hukumar zaben ta bullo da su, inda ya ce, “Wanda duk ya kawo kati na’urar za ta iya hakikancewa idan katin nasa ne; na’urar karama ce kamar wayar mobile haka; za ta fito da hoto na sunan mutum. Duk wanda yak e nan kusa zai ji ko an tantance ko ba a tantance ba – ‘yan siyasanmu a ba mutum kati sai a saye katin ranar zabe kuma a bai wa wani ya yi zabe da shi; to insha Allahu yanzu kam ko sun sai kati ba za su iya amfani da shi ba; saidai idan wanda su ka sai katin nasa kuma shi ma sun sayo shi ya zo da katin ya zabe su saboda idan ba haka ba katin ba zai yi amfani ba.
Nasiru ya ruwaito Mataimakin Kakakin kampe na Jonathan Isah Tafida Mafindi na cewa ba da magudi PDP ta rinka lashe zabe tun daga 1999 ba, kuma ya na da kwarin gwiwar wannan karon ma za ta sake samun nasara. Saidai kuma Gwamnan Nasarawa na APC Tanko Almakura na ganin za a samu sauyin shugabanci wannan karon.