Farfesa Jega yace “a halin yanzu dai, gaskiya yadda al-amuran kasar mu suke, da kuma irin matsalolin da muke fuskanta wurin yin zabe, zai yi wahala ayi zabe biyar duk a rana daya. Gaskiya abu ne wanda yake da wahala”.
Mr. Keyen ya tambaye Farfesa Jega ko kalubalen gudanar da zaben ne yasa ba’a samun nasara a zabubbukan Afirka.
“Musamman yana da alaqa da abubuwan da ake bukata a samu nasarar zabe duk a rana daya. Misali in ka lura ai, tun shekara ta 2011 zaben da aka yi, har ila yau korafin da ake yi shine, ba’a fara zabe akan lokacin. Kuma wannan ya danganci yawan mutanen da zaka aika, da yawan kayan aikin da za’a tura. Don haka in kace zaka zo kayi duk zabubbukan a rana daya, to gaskiya wato, abunda ake bukata ayi wannan yana da yawa kwarai da gaske. Don haka sannu a hankali, zamu yi ta kokari mu ga har an kai wannan lokacin, amma dai a halin yanzu, gaskiya zai yi wuya. Baza a iya ba, kuma muna gani illarsa zai fi amfaninsa yawa."
"Baza mu iya yin duka a rana daya ba, amma a maimakon sau uku, meyasa baza mu mayar da shi sau biyu ba? To abunda yasa muka ce to lallai zamu iya hada zaben shugaban kasa, da na ‘yan majalisa. Sai ayi. Kuma wadannan zabubbuka ne wadanda ake yi na tarayya, na kasa, sannan akwai zabubbuka wadan ake yi na jiha, wato na gwamna, da kuma ‘yan majalisar jiha. Don haka, kaga tsarin ba zai yiwu ba idan ka dauko na ‘yan majalisar jiha, ka hada shi da na gwamna.”
“Akasari a duk duniya, inda ake zabe kashi kashi, ana raba zaben kasa, da na tarayya, da kuma na jiha. To shiyasa muka ga cewa, to tunda muna so mu mayar da shi biyu, ai bari mu fara mu hada da na shugaban kasa, da na ‘yan majalisar tarayya.”
Shugaban sashen Hausa ya tambayi Farfesan ko fara zaben shugaban kasan, zai saka mutane suyi zargin cewa an shirya haka ne don wanda ya ci shugabancin kasa yayi amfani da wannan dama wajen tursasa wa ragowar ‘yan siyasa bin ra’ayoyinsa.
Mr. Jega yace “kasan yanayin aikin namu yadda yake, duk abinda zaka yi, sai an samu kace-nace da korafi. Mu dai Allah Ya sani, kuma a zuciyar mu, mun tabbatar cewa mun yi wannan abun ne don muga yaya za ayi a kara inganta al amari na zabe. Bamu yi shi da wata niyya ba, ko don a cutar wa wani, ko kuma don a taimaka wa wani. Wannan shine gaskiyar al-amari.”