Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Buhari Na gaba a Kidayar Kuri'u


Dan takarar shugaban kasar jam'iyar APC, Janar Muhammadu Buhari
Dan takarar shugaban kasar jam'iyar APC, Janar Muhammadu Buhari

Yayin da ake ci gaba da kidayar kuri'u a Najeriya, rahotanni daga kasar na nuna cewa dan takarar shugaban kasa na APC Muhammadu Buhari ne a gaba.

Sakamakon baya baya da aka samu na zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya ya nuna cewa abokin hamayyar shugaba Goodluck Jonathan, Janar Mohammadu Buhari mai ritaya shi ke kan gaba duk da cewa akwai ‘yan jihohin da suka rage ba a kirga ba.

Jumullar sakamakon da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta fidda, ya nuna cewa Buhari yayi nasara a jihohi da yawa fiye da shugaba Jonathan, inda yake kan gaba da kuri’u kusan miliyan 3 a fadin kasar.

Mohammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya lashe zaben a jihohi akalla 6 dake kudancin kasar, jihohin da aka again kamar shugaba Jonathan ya fi karfi.

Samun nasarar Buhari, za ta kawo karshen shekaru 16 da jam’iyyar shugaba Jonathan ta PDP ta kwashe ta na mulki, abin da kuma zai mai da shi Buharin kan karagar mulki tun bayan shekaru 30 da suka wuce.

Janar Buhari mai ritaya, dan shekaru 72 da haihuwa, yayi mulki a kasar a lokacin soja a aluf dari tara da tamanin da hudu zuwa aluf dari tara da tamanin da biyar. Biyo bayan wani juyin mulki da aka yi.

Sai dai idan shugaba Goodluck ya lashe zaben hakan na nufin jam'iyar ta PDP za ta ci gaba da mulkar kasar tun bayan da Najeriyar ta koma mulkin dimokradiya a shekarar 1999.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG