Ra’ayoyi Mabanbanta Kan Nada Buhari Jagoran Yaki Da Cin Hanci a Afirka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya

Nadin da aka yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a matsayin jagoran yaki da cin hanci a nahiyar Afirka, ya janyo suka da yabo daga jama'a da dama.

Bayan da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka na AU, ya zabi shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a matsayin jagoran yaki da cin hanci a nahiyar Afirka, ana ta bayyana ra’ayoyi mabanbanta.

A taronta da ta gudanar a karo na 30 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wanda aka kammala a yau Litinin, kungiyar ta AU ta zabi shugaba Buhari a matsayin jagora.

Rahotanni sun ce an zabe shi ne, saboda rawar da ya taka wajen rage matsalar cin hanci a Najeriya tun bayan da ya hau mulki.

Koda wasu na ganin akasin hakan, lura da cewa har Najeriyar ba ta tsira daga wannan matsala ba.

Nahiyar Afirka, na fama da matsaloli da suka hada da cin hanci, wanda aka yi kiyasin cewa ita take janyo koma baya ga yankin.

To sai dai yayin da wasu ke yaba wannan zabi na shugaba Buhari, wasu na nuna akasin hakan.

Saurari wannan rahoto na Hassan Maina Kaina da ya tattauna da masu fashin baki kan dalilan daukar matsayarsu:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyi Mabanbanta Kan Nada Buhari Jagoran Yaki Da Cin Hanci a Afirka - 2'48"