Babachir dai wanda da alamu yaje hedikwatar hukumar tun a safiyar Laraba sai jami’an suka rike shi, don yi masa tambayoyi kan tuhumar da ake yi masa, ciki har da batun aringizon kudi a kwangilolin sake tsugunnar da al’ummar Arewa maso gabashin Najeriya.
Mukaddashin jami’in labarun hukumar Samin Amadin, ya ce za a ci gaba da yiwa Babachir tambayoyi a Alhamis din nan, yana mai cewa sam kamawa ko tsare Babachir bata da alaka da wasikar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar.
Idan za a tuna binciken Babachir Lawal da kwamitin Majalisar Dattawa yayi ya kai karkatar da Biliyoyin Naira. Inda shugaban kwamitin yace sun gano cewa anyi almubazzaranci na fiye da Naira Biliyan takwas.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum