Akalla shanu 73 wasu mahara suka kashe a kauyen Kadarko da ke karamar hukumar Keana na jihar Nasarawa a arewacin Najeriya.
Rundunar ‘yan sanda jihar ta Nasarawa wacce ta tabbatar da aukuwar harin ta ce, wasu mutane biyu sun bata bayan da maharani suka far wa kauyen, inda suka yi ta harbi akan mai uwa-da- wabi.
“Wasu ne suka bude wuta akan shanu, hakan ya yi sandin mutuwar shanu 73, sannan 18 suka samu rauni.” Inji Kakakin ‘yan sanda jihar ta Nasarawa, ASP Kennedy Idris.
Ya kuma kara da cewa, wasu mutane shida sun bata a lokacin harin, amma an yi nasarar gano mutum hudu yana mai cewa har yanzu ba a kama kowa ba.
“Yanzu dai an fara bincike, amma ba a samu an kama kowa ba.” Ya kara da cewa.
Rikicin manoma da makiyaya ya haddasa asarar rayuka a wasu sassan Najeriya, musamman a yankunan Taraba da Benue da Pilato da kuma jihar ta Nasarawa.
Lamarin ya kai ga har shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci shugaban ‘yan sandan kasar ya tare a jihar Benue.
Sannan ya kuma gana da shugabannin jihar ta Benue a wani mataki na neman masalaha.
Rahotannin baya bayannan na nuni da cewa gwamnatin tarraya, na duba yiwuwar aike wa da sojoji zuwa yankunan da ake yawan samun rikice-rikice.
Ana duba yiwuwar daukan wannan mataki kamar yadda jaridun Najeriya da dama suka ruwaito, domin a dakile hare-haren da ake zargin wasu gugun mahara ke kai wa a sassan kasar.
Kwamitin da Fadar shugaban Najeriya ya kafa a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbanjo ne ya bayyana yiwuwar tura sojoji zuwa yankunan kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyanawa jaridar Vanguard.
Kwamitin har ila yau na dauke da wasu gwamnoni tara na Najeriya.
Saurari rahoton Zainab Babaji domin karin bayani:
Facebook Forum