Baya ga kira ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yar da kwallon mangwaron ya huta da kuda a zabe mai zuwa, wani abu mai janyo takaddama a wasikar da tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta a wasikar shi ne batun kafa wani abu mai kama da jam’iyya ko kuma a kalla kungiyar siyasa. Tuni wasu masu fassara ke ganin Obasanjo ya yi jirwaye ne mai kamar wanka a wani yinkurin na ganin an kafa wata sabuwar jam’iyyar siyasa. Hasalima, jaridar Premium Times ta yanar intanet ta nuna cewa Obasanjo na magana ne a fakaice game da wani shiri na kafa wata jam’iyyar siyasa a karshen wannan wata a Abuja, karkashin tsohon gwamnan Osun Olagunsaye Oyinlola.
Mai bai wa Shugaban Najeriya Shawara kan Labarai Garba Shehu, ya ce wasikar ta Obasanjo ta taba al’amura da dama, ciki har da wasu da gwamnatin ta Buhari ke ganin shawara ce da ka iya zama mai kyau kuma za a duba a gani. Shehu ya ce Shugaba Buhari ba ya fushi da kowa kan wannan wasikar saboda, a cewarsa, gwamnatin Buhari mai sauraron shawara ce.
A wani bangaren kuma, wani wanda ya dade da bibiyar siyasar Obasanjo mai suna Isa Tafida Mafindi ya ce ya na ganin Obasanjo ya kula cewa ‘yan APC na fama da yinwa kuma PDP ta yi lalacewar da gyararta abu ne mai wuya.
Ga dai wakilinmu Nasiru Adamu Elhikya da cikakken rahoton:
Facebook Forum