Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwankwaso Ya Janye Shirinsa Na Kai Ziyara Kano


Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya janye kai ziyara Kano domin gudun aukuwar rikici a jihar.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya janye shirinsa na kai ziyara jihar kamar yadda ya shirya.

Tsohon sakataren kwankwaso a zamanin mulkinsa, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichine ne, ya bayyana hakan, inda ya ce hakan ya biyo bayan shawarwarin da aka ba shi kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ta wallafa a yau.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa, "Na janye ziyarata zuwa Kano bayan jin shawarwarin ‘yan Najeriya a gida da waje domin kaucewa rikicin siyasa a jihar da ka iya biyo baya."

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Rabiu Yusuf, ya sanar wa manema labarai cewa, bayanan sirrin da suka tattara, sun nuna cewa wasu tsageru na yunkurin ta da fitina a yayin ziyarar.

Hakan ya sa ta shawarci tsohon gwamnan ya dage ziyarar zuwa lokacin da lamura za su daidaita.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG