Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Ta Mayar wa Da Obasanjo Martani


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Ministan yada labarai a Najeriya, Lai Muhammed, ya mayar wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo martani kan kalaman da ya yi game da kalaman da ya yi kan shugabancin Buhari da kuma batun kada ya tsaya takara.

Gwamnatin Najeriya ta mayar wa da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo martani bisa kalamansa na cewa Shugaba Buhari ya gaza kuma kada ya tsaya takara a zaben shekarar 2019.

Sahfin yanar gizon gidan talbijin na Channels, ya wallafa wata sanarwa da Ministan yada labarai Lai Muhammed ya fitar yana cewa,"mun samu jawabin Olusegun Obasanjo akan halin da kasar take ciki."

Lai Muhammed, ya yaba da kishin kasa da Obasanjo ya nuna, yana mai gode masa da har ya ambato cewa an samu ci gaba a fannin yaki da ta'addanci da rashawa.

Sai dai sanarwar ta ce bisa ga dukkan alamu tsohon shugaban bai ambato abubuwan da wannan shugaban ya yi baki daya ba.

Lai Muhammed ya tunawa Chief Obasanjo wasu muhimman abubuwan da Shugaba Buhari ya yi ya kuma ci nasara.

Ya ce akwai batun kaddamar da asusu daya na gwamnatin, wanda a cewar Lai Muhammad ya tanada wa kasar kudi sama da Naira biliyan 108 wanda hakan ya sa kudaden shiga suka karu.

Sannan ya ce kasuwar saka hannayen jari ta kasar tana cikin wadanda suka fi inganci a duniya, baya ga haka, bankin duniya ya ayyana Najeriya cikin kasashen da suka fi saukin yin kasuwanci.

Minista Lai Muhammed ya kara da cewa aikin noma ya habaka har ma Najeriya ce take samar da kaso 70 cikin 100 na doyar da ake shukawa a duk fadin duniya.

Da ya koma kan fannin jin dadin jama'a, Lai Muhammad, ya ce 'yan makaranta miliyan 5.2 a makarantun firamare 28,249 a jihohi 19 ne ake ciyar da su.

Sannan an samar wa da matasa masu digiri fiye da 200,000 aikin yi, kana, wutar lantarki ta karu zuwa karfin megawat 7,000.

Har ila yau, Muhammed ya ce, an samu a ci gaba da gina layin dogo tsakanin Lagos da Kano da kuma Kano zuwa Kaduna.

A cewar Lai Muhammed manufar gwamnatin ita ce ta kewaye kasar da layin dogo nan da zuwa shekarar 2021.

Kazalika gina hanyoyin motoci na ci gaba, a cewarsa.

Akan ko shugaban ya sake tsayawa takara, ministan ya ce, wannan wani shiri ne na raba hankalinsa daga ayyukan da yake yi.

Shugaban ya dukufa wajen cika wa 'yan Najeriya alkawuran da ya yi masu a shekarar 2015 kamar yadda shafin yanar gizon na gidan Channels ya ruwaito.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG