A ranar Juma’a kasar Pakistan ta sanya tsauraran matakan tsaro a cikin da wajen Islambad, don hana magoya bayan tsohon firai minista Imran Khan da aka daure yin maci a babban birnin kasar.
Hukumomin kasar sun rufe manyan tituna da hanyoyi shiga cikin birnin da kwantenonin jigilar kaya.
Sun dakatar da sabis na wayar salula, rufe makarantu da hada-hadar sufurin jama’a na hukuma.
Ministan Harkokin cikin gida na Pakistan Mohsin Naqvi ya ce, “babu wanda ya yi farin cikin rufe birnin tare da kwantenonin jigilar kaya, kuma mutane suna fuskantar matsaloli, amma dole ne mutane su fahimci dalili da yasa muke yin haka, kuma saboda wanene, kuma me yasa.”
An jibge jami'an ‘yan sanda da dakaru sa kai a wuraren shiga da fita, kuma gwamnati ta dakatar da taron jama’a na wani dan lokaci a Islamabad.
Haka kuma an sanya irin wadannan matakan tsaro a birnin Rawalpindi da ke makwabtaka da shi, inda hedkwatar sojojin Pakistan ta ke.