A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi a Islamabad, ma’aikatar harkokin wajen kasar, ba tare da ambatar sunan dan wata kasa ba, ta bayyana maharan a matsayin “gungun masu tsatstsauran ra’ayi” sannan ta koka kan yadda aka keta tsaron karamin ofishin jakandancin, tana mai cewa hakan ya jefa rayuwar ma’aikatanta cikin hadari.
“Muna isar da matukar adawar mu ga gwamnatin Jamus,” in ji Ma’aikatar.
Ta bukacin Jamus da ta dauki “matakan gaggawa don sauke nauyin da ke kanta” karkashin yarjejeniyar Taron Vienna kan huldar jakadanci, don tabbatar da tsaron ofisoshin jakadanci da ma’aikatan Pakistan a cikin kasar.
Wani faifan bidiyo na abun da ya faru da aka yada a kafafan sada zumunta ranar Asabar, ya nuna mutane da dama rike da tutar kasar Afghanistan, mai launin kaloli uku, suna tsallaka katanga don shiga ginin karamin ofishin jakadancin da ke Frankfurt, inda daya daga cikinsu ya sauke tutar Pakistan.
Rahotannin sun ce masu zanga zangar na ta fadan kalaman cin zarafi tare da jifan ofishin jakadancin da duwatsu.
Majiyoyin diflomasiyya da shaidu a birnin na Jamus sun tabbatar wa da VOA sahihancin bidiyon, sai dai nan take ba’a san a kan abun da mutanen ke zanga zanga a kai ba.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Jamus dangane da harin da aka kai da kuma Allah wadai da Paksitan ta yi.
Dandalin Mu Tattauna