Jami’an tsaro sun tabbatar wa Muryar Amurka mutuwar, inda suka ce harin ya afku ne a lungu da sako na Tirah da ke arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa sannan kuma ya yi sanadin jikkatar sojoji shida.
Bangaren yada labarai na rundunar sojin Pakistan bai amsa bukatar Muryar Amurka nan take ba kan harin da aka kai a tsohuwar tungar mayakan da ke kan iyakar Afghanistan.
Mayakan da ke da alaka da haramtacciyar kungiyar Taliban ta Pakistan, wadanda aka fi sani da Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP), sun fitar da wata sanarwa inda suka dauki alhakin kai farmakin a Tirah.
Mummunan harin dai ya zo ne kwana guda bayan da rundunar sojin Pakistan ta bayar da rahoton cewa, wani harin ta'addanci da aka kai kusa da babban birnin lardin Peshawar ya kashe sojojin Pakistan biyu da wasu biyar da ake zargin 'yan ta'adda ne da ke da alaka da TTP.
Ministan cikin gida na Pakistan Mohsin Naqvi ya bayyana cewa, TTP ce ta shirya tare da ba da umarni daga matsugunan Afganistan, wani harin kunar bakin wake da aka kai a Khyber Pakhtunkhwa a cikin watan Maris din da ya gabata wanda ya kashe injiniyoyin China biyar tare da direbansu, wani dan Pakistan. A lokacin da lamarin ya faru, ‘yan kasar China na aikin ne a wani babban aikin samar da wutar lantarki a lardin da ake kira Dam Dasu.
Dandalin Mu Tattauna