Hatsarin ya faru ne a daren Talata a Lardin Yazd da ke tsakiyar kasar Iran, in ji Mohammad Ali Malekzadeh, wani jami'in agajin gaggawa na kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya bayyana.
Ya kara da cewa wasu mutane 23 sun samu raunuka a hatsarin, kuma 14 daga cikinsu masu tsanani. Ya ce dukkan fasinjojin bas din sun fito ne daga Pakistan.
Akwai mutane 51 ne a cikin motar bas din a lokacin da hadarin ya afku a wajen birnin Taft mai tazarar kilomita 500 kudu maso gabashin Tehran babban birnin kasar Iran.
Hukumomi a Pakistan sun bayyana wadanda ke cikin motar bas din da cewa sun fito ne daga birnin Larkana da ke lardin Sindh na kudancin Pakistan.
-AP
Dandalin Mu Tattauna