Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amurka Sun Bankado Yunkurin Wani Dan Kasar Pakistan Na Kashe Amurkawa


Asif Merchant
Asif Merchant

Da alama wata makarmashiyar Iran ta kashe tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na da nasaba da yunkurin wani dan Pakistan mai alaka da Tehran na niyar kaiwa wasu manyan 'yan siyasa da jami'an Amurka hari.

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta bayyana tuhume-tuhume da ake yi wa wani dan Pakistan mai alaka da Tehran

Asif Merchant mai shekaru 46, wanda ya shiga Amurka a cikin watan Afrilun wannan shekarar ne da nufin neman sojojin haya da zasu kashe mutane da dama.

Sai dai a cewar karar da yunkurin Mechant ya gamu da cikas ne bayan mutumin da Merchant ya tuntuba a kokarinsa na aiwatar da shirin ya tuntubi jami’an tsaro.

Ba a bayyana wadadanda Mechant ya ke niyar kashewa a bayanan da aka gabatar a New York ba, amma bayanan na zuwa ne makonni kadan bayan da jami'an Amurka suka ce sun kara tsawata tsaro ga tsohon Shugaban saboda barazanar da ke da alaka da Tehran.

Bayanin da aka fitar jiya Talata shi ne na baya-bayan nan a jerin makarkashiyar ta aka dakile na kashe Amurkawa da sauran makiyan Iran a kasar Amurka.

A watan Janairun da ya gabata, Amurka ta tuhumi wasu mutane uku, daya daga cikinsu yana zaune a Iran, a yunkurin kashe wasu Amurkawa biyu a jihar Maryland.

Amurka ta kuma shigar da kara a yunkurin kashe Masih Alinejad, wani Ba’amurke dan asalin kasar Iran, dan fafutukar kare hakkin bil’adama kuma mai gabatar da shirin talabijin na Muryar Amurka a harshen Farsa.

Yawancin barazanar da aka yi a baya-bayan nan, gami da wadanda ke kaiwa Bolton da Trump hari, sun samo asali ne daga sha'awar Tehran na neman daukar fansa kan harin jirgin da baya amfani da matuki da Trump ya umarta a watan Janairun 2020 a Bagadaza wanda ya kashe Qassem Soleimani, shugaban Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran.

Lauyan da kotu ta nada wa wadanda ake kara a kan makarkashiyar kashe Trump, da sauran su, ya ki cewa komai lokacin da Muryar Amurka ta tuntube shi.

Sai dai takardun cajin na zargin Merchant ya yi balaguro daga Pakistan zuwa Turkiyya sannan kuma ya je birnin Houston na jihar Texas a watan Afrilu, bayan ya shafe kusan makonni biyu a Iran.

Da ya sauka a Amurka, masu shigar da karar sun ce, nan da nan Merchant ya fara neman mutane domin su taimaka masa da aiwatar da shirin, inda ya shaida wa wanda ya sanar da jami’an tsaron cewa, zai iya samun kudi har dalar Amurka 100,000 kuma abinda zai shafi mutane da dama.

An tuhumi Merchant da bai wa wasu jami’an tsaro farin kaya biyu da suka badda kama da laifin cin hanci da rashawa na dala $5,000 a karshen watan Yuni don aiwatar da shirin, inda ya yi masu alkawarin cewa zai kara masu kudi bayan ya dawo daga Pakistan.

Jami’an tsaro na Amurka sun kama Merchant a ranar 12 ga watan Yuli, kafin ya iya barin Amurka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG