Daga karshe dai Hamas ta bayar da sunayen, kuma Isira’ila ta ce za a fara tsagaita wuta da karfe 11:15 na safe.
Da yammacin ranar Asabar TikTok ya daina aiki a Amurka, kuma ya bace daga shagunan manhajojin Apple da Google, gabanin dokar da za ta fara aiki ranar Lahadi da ta bukaci a rufe manhajar da Amurkawa miliyan 170 ke amfani da ita.
Isra’ila ta ba da sanarwar ficewa ta gargadin ga mazauna Baalbek a gabashin Lebanon a rana ta biyu a jere.
Gachagua shi ne mataimakin shugaban kasa na farko da aka taba tsigewa a tarihin Kenya.
Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke kai hari kan mayakan Hezbollah a Lebanon da sabunta hare-haren da take kai wa kan Hamas a arewacin Gaza.
Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin makarantar.
Hashem Safieddine, dan uwan ne ga Nasrallah kuma babban jami’in kungiyar ne da ake sa ran zai maye gurbin Nasrallah
Shugaban mai shekaru 66 da haihuwa ya fada a cikin wani jawabi a hedkwatar yakin neman zaben sa cewa, “Za mu tsarkake kasar daga dukkan masu cin hanci da rashawa da kuma mazambata.”
Ya shaida wa manema labarai cewa, “Batun da ya fi muhimmanci a yau shine tsagaita wuta, musamman a Lebanon da kuma Gaza.”
Firai Ministan Garry Conille ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, “Za’a farauto wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya, ba tare da bata lokaci ba.”
Hukumomin kasar sun rufe manyan tituna da hanyoyi shiga cikin birnin da kwantenonin jigilar kaya.
Domin Kari