Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum 50 Sun Mutu Bayan Hare-haren 'Yan bindiga A Pakistan


Balochistan, Pakistan Agusta 26, 2024
Balochistan, Pakistan Agusta 26, 2024

Hare-haren 'yan awaren akan ofisoshin 'yan sanda, layin dogo da manyan tituna a Lardin Balochistan da ke Pakistan, tare da daukar fansa da jami'an tsaro suka yi, sun hallak akalla mutane 51, kamar yadda jami'ai suka sanar a ranar Litinin.

Hare-haren da masu tayar da kayar baya na kabilanci suka fi yaduwa cikin shekaru, wani bangare ne na kokarin da aka kwashe shekaru ana yi na samun nasarar ballewa daga lardin kudu maso yammacin kasar mai arzikin albarkatun kasa, inda ake gudanar da manyan ayyukan da kasar Sin ke jagoranta, kamar tashar jiragen ruwa mai dabaru, da ma'adinin zinari da tagulla.

Kahuta, Pakistan
Kahuta, Pakistan

"Wadannan hare-haren dai da aka yi cikin tunanin na musamman ne don haifar da rikici a Pakistan," in ji ministan harkokin cikin gida Mohsin Naqvi a cikin wata sanarwa, inda ya kara da cewa jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda 12 a farmakin da suka kai bayan harin, amma ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Mafi girman hare-haren an auna motoci ne daga bas zuwa motocin manyan kaya a kan babbar hanya, inda suka kashe akalla mutane 23, in ji jami'ai, tare da kona motoci 35.

Balochistan, Pakistan
Balochistan, Pakistan

An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa tare da Quetta sakamakon fashewar wasu abubuwa a kan gadar jirgin kasa da ta hada babban birnin lardin da sauran kasar Pakistan, da kuma hanyar layin dogo zuwa makwabciyarta Iran, in ji jami'in kula da harkokin jiragen kasa Muhammad Kashif.

Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG