Kanar Assimi Goita ya hambaras da gwamnatin Ndau.
Shi kansa shugaban sojojin juyin mulkin, Kanar Goita ya tsallake rijiya da baya bayan da akai yunkurin halaka shi yayin da yake sallar jummu'a a wani masallaci da ke Bamako, babban birnin kasar.
A Kasar Guinea, nanma wani matashin soja dan kimanin shekaru 43, Kanar Mamadi Dambouya ya jagoranci juyin mulkin da ya hambaras da gwamnatin demokradiyya ta shugaba Alpha Conde.
Ranar ashirin da biyar ga watan Oktoban 2021, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Sudan, Laftanar Janaral Abdel Fatah Alburhan ya hambaras da gwamnatin rikon kwarya da ke karkashin jagorancin Abdallah Hamdok.
Bayan dai kokawar neman mulki, mummunan rikici ya barke tsakanin Janar Alburhan da mataimakinsa Janar Mohammed Daglo, rikicin da a halin yanzu ke ci gaba da tarwatsa kasar ta sudan da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu biyar cikin wata biyar.
A Burkina Faso, wani matashin hafsan soja dan kimanin shekaru 34, Laftanar kanar Ibrahim Traore ya fatattaki gwamnatin demokradiyya ta shugaba Henry Sandaogo Damiba a watan satumban bara, Kanar Traore dai a halin yanzu shine shugaban kasa mafi karancin shekaru a duk duniya.
A karshen watan jiya ne kuma kwamandan askarawan da ke tsaron fadar shugaban kasa a Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourrahmane Tchiany su ka hambaras da shugaba Bazoum Muhammad.
A wani abu mai kama da arashi kuma, suma sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa a Gabon karkashin jagorancin Kanar Brice Clotaire Oligui Nguema ya jagoranci juyin mulkin da ya hambaras da Shugaba Ali Bongo.
Kwararre kan kimiyyar siyasa Dr. Sa'idu Ahmad Dukawa na cewa tsananin rayuwa da matsalar tattalin arziki da magudin zabe da dadewar shugabanni a kan mulki na daga cikin dalilan da ke jawo yawan juyin mulkinnan.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5