Mutum 36 Sun Mutu, Dubbai Na Tserewa Gobarar Da Ta Tashi A Hawaii

APTOPIX Gobara a da ta lake e garin Maui, Hawaii - Amurka

Dubban mazauna Hawaii ne suka dinga tserewa daga gidajensu a Maui yayin da wata gobara ta mamaye tsibirin, inda ta lalata sassan wannan gari da ya shafe shekaru aru-aru tare da kashe akalla mutum 36 a wata gobarar daji mafi muni da Amurka ba taba gani ba a shekarun baya-bayan nan.

WASHINGTON, D.C. - Gobarar ta shammaci mazauna tsibirin, inda ta bar motoci da suka kone a kan titunan da, da ake gani cike da cunkoson jama'a da kuma tarin baraguzan gine-gine a garin Lahaina, wanda ya kasance mai shekarun tun 1700 kuma ya kasance wurin da 'yan yawon bude ido suka fi so a Hawaii.

Hayaki na tashi daga gobara a Lahaina, gundumar Maui

Ma’aikatan kashe gobara sun yi ta kokarin shawo kan gobarar a wurare da dama a tsibirin ranar Laraba, kuma har wutar ta tilastawa wasu manya da kananan yara tserewa cikin teku.

Akalla mutum 36 ne suka mutu, a cewar wata sanarwa daga gundumar Maui da yammacin Larabar da ta ce babu wasu bayanai da aka samu. Jami'ai dai sun ce tun da farko gobarar ta lalata gine-gine 271 tare da jikkata mutane da dama.

Magajin garin Maui Richard Bissen Jr. ya ce wannan wani gwaji ne akan tsibirin kamar yadda ba a taɓa samun irinsa ba a rayuwarmu.

"Muna bakin ciki da yi wa juna jaje a wannan lokaci mara dadi," in ji shi a cikin wata sanarwa da aka yi rikodi. "A cikin kwanaki masu zuwa, za mu yi samu karfin guiwa a matsayin 'Kaiaulu,' wato Al'umma da harshen Hawaii, yayin da muke sake ginawa tare da juriya da Aloha, wato maraba ko gaisuwa da harshen Hawaii."

Mutane da masu yawon bude ido a tashar jirgin sama suna kokarin tserewa gobarar da take lakume garin Maui, Hawaii

Yayin da gobarar ta tashi, an shawarci masu yawon bude ido da su kauracewa yankin.

Kimanin maziyarta 11,000 ne suka tashi akan jirgi daga Maui ranar Laraba, inda ake sa ran akalla wasu 1,500 za su bar garin a ranar Alhamis, a cewar Ed Sniffen, darektan sufuri na jihar.

Jami'ai sun shirya Cibiyar Taro ta Hawaii Convention Center don daukar dubunnan mutanen da suka yi gudun hijira.

-AP