Fashewar da ta tashi a wani shahararren gidan rawa ta kuma raunata mutane takwas.
Gwamnati na kira da a kwantar da hankali yayin da dubban magoya bayan kwallon kafa suka ziyarci Yaounde domin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi.
Daruruwan mutane ciki hada da jami'an gwamnatin Kamaru sun fito Bastos da ke unguwar Yaounde a safiyar Lahadi, sun cika sunna kallon yadda makwabta da ma'aikatan Livs, wani sanannen gidan rawa da hukumar kashe gobara ta kasar Kamaru, ke binciken wasu gine-gine uku da suka kone a yankin.
Daga cikin fararen hula da suka taimaka wajen neman wadanda suka jikkata har da Gustav Lemaleu mai shekaru 27.
Lemaleu ya ce fararen hula da hukumar kashe gobara na ma'aikatar Kamaru sun ceci rayukan mutane akalla 40.
Ya ce yana da wuya a san sunaye da kuma kasashen wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu saboda ba sa gabatar da takardun shaida kafin samun damar shiga Livs.
Lemaleu ya ce yana da tabbacin cewa wadanda abin ya shafa sun hada da mutanen da suka ziyarci Kamaru domin halartar gasar cin kofin Afrika da ake yi.
A wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce gobarar na gidan rawan dare ta bazu zuwa wani kantin sayar da iskar gas. An yi tashin bama-bamai masu karfi daga tankunan gas guda shida, lamarin da ya haifar da firgici a unguwar.
Ministan kiwon lafiyar jama'a Manaouda Malachie ya ce shugaba Paul Biya ya umarci ma'aikatan lafiya da su kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Yaounde kuma a yi musu magani kyauta.
Shugaba Biya ya yi kira da a kwantar da hankula tare da ba 'yan wasan kwallon kafa, magoya bayanta da jami'an wasannin da ke halartar gasar cin kofin Afrika a Yaounde tabbacin kare lafiyarsu.
Kasar Kamaru dai na karbar bakuncin dubban jama'a ne da ke halartar gasar AFCON da aka fara a ranar 9 ga watan Janairu, wanda za a kammala gasar a ranar 6 ga watan Fabrairu.