Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji
Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

Hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka a ranar Laraba, ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.

WASHINGTON, D.C. - Ya kuma hana jiragen sama tashi a manyan filayen jirgin sama, da dage wasannin kwallon Baseball inda kuma mutane suka koma sanya takunkumin rufe fuska kamar a lokacin annobar COVIDD-19.

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji
Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

Jami'an Canada sun nemi karin taimako daga wasu kasashe domin yaki da harsunan wuta fiye da 400 da ke ci a fadin kasar da tuni suka raba mutane 20,000 da muhallansu. Gurbataccen iska mai haɗari ya bazu zuwa yankin birni New York, tsakiyar jihar New York da sassan Pennsylvania da New Jersey. Manyan giza-gizan gurbataccen iskar ya bazu har zuwa Arewacin jihohin Carolina da Indiana, ya kuma shafi miliyoyin mutane.

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji
Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

Jami'an Canada sun ce lamarin na rikidewa zuwa gobarar daji mafi muni da aka taba samu a kasar. Ta fara ne da farko akan busasshiyar ƙasa fiye da yadda aka saba kuma ta yi saurin bazuwa sosai, ta karar da kayayyakin kashe gobara a duk faɗin ƙasar, da kuma gajiyar da masu kashe gobarar, in ji jami'an kashe gobara da muhalli.

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji
Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

Mai magana da yawun cibiyar kashe gobarar daji ta Canada, Jennifer Kamau, ta ce sama da ma’aikatan kashe gobara 950 da sauran jami’an kashe gobara sun iso daga Amurka, Australia, New Zealand da Afirka ta Kudu, kuma za a sami karin wasu nan ba da dadewa ba.

In Washington, White House press secretary Karine Jean-Pierre said President Joe Biden has sent more than 600 firefighters and equipment to Canada. His administration has contacted some U.S. governors and local officials about providing assistance, she said.

Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji
Miliyoyin Mutane A Canada Da Amurka Suna Shakar Gurbatacciyar Iska Sakamakon Gobarar Daji

A birnin Washington, sakatariyar yada labaran fadar White House Karine Jean-Pierre ta ce shugaba Joe Biden ya aike da jami'an kashe gobara da kayan aiki sama da 600 zuwa kasar Canada. Gwamnatinsa ta tuntubi wasu gwamnonin Amurka da jami’an yanki kan samar da taimako, in ji ta.

-AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG