WASHINGTON, D.C. -Hotuna daga wurin da gobarar ta tashi sun nuna jerin gawarwaki dake kwance a wajen cibiyar dake garin Ciudad Juarez, daga El Paso a jihar Texas. Sannan an ga motocin daukar marasa lafiya, da ma'aikatan kashe gobara, da ma manyan motocin daukar gawarwaki a wurin.
Mutane 39 ne suka mutu yayin da 29 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi da yammacin ranar Litinin, kamar yadda wani jami’in hukumar kula da shige da fice ta kasar ya bayyana, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba su izinin yin magana a kan batun ba.
Birnin Ciudad Juarez wani babban mashigi ne da bakin haure ke ratsawa su shiga Amurka. Cibiyoyin tsugunnar da jama'a na birnin na cike da baki da ke jiran samun damar tsallakawa ko kuma wadanda suka nemi mafaka a Amurka dake jiran bin tsarin.
Ofishin babban lauyan Mexico ya kaddamar da bincike kuma ya tura masu bincike a wurin da gobarar ta auku, kuma an kira Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa don taimakawa bakin hauren, a cewar rahotannin kafafen yada labarai.
-AP