Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto: Ibtila’in Gobara Ya Abka Wani Gidan Siminti Da Ke Ajiyar Man Gas


GOBARA
GOBARA

A Najeriya jama'ar kasar na ci gaba da fuskantar wasu matsaloli da ke sanadin salwantar rayukan jama'a ta fuskoki daban daban, kamar yadda wata gobara da ta kama wani kamfanin siminti ta yi sanadin salwantar rayuka a Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar.

A wurin ‘yan Najeriya, jin labarin wani abu ya yi sanadin salwantar rayuka ba bakon abu bane, sai dai yadda abin ya faru kan iya nuna yanayin alhinin jama'a akan rashin.

Wannan karon wani ibtila'i ne ya faru a daya daga cikin gidajen yin siminti na kamfanin BUA na Najeriya, inda gobara ta kama a wurin ajiye man gas a gidan siminti na kamfanin dake Sakkwato.

GOBARA
GOBARA

Gobarar, wadda ta kama ranar Jumu'ar da ta gabata ta yi sanadin hasarar rayukan wasu mutane.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin kamfanin sai dai abin ya faskara, amma dai ya fitar da wani bayani a rubuce wanda aka bai wa manema labarai wanda ke dauke da sa hannun mataimakin daraktan kula da harkokin mulki Sada Sulaiman wanda a cikin kamfanin ya tabbatar da mutuwar mutane uku da ke aiki dab da inda gobarar ta tashi.

Bayanin da kamfanin ya fitar ya nuna cewa jami'an kashe gobara na hadin gwiwa da jami'an kamfanin wajen kokarin shawo kan lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton akwai maso-mason wutar kuma jami'an na kashe gobara na kula da lamarin.

Duk da ya ke bayanin da kamfanin ya fitar ya ce har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, wasu na ganin aikin walda ne ake yi wurin kafin gobarar ta kama.

Shi dai wannan kamfanin siminti da ke shiyyar kalambaina, ranar 27 ga watan Janairun wannan shekara ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yi tattaki har zuwa Sakkwato domin kaddamar da bude wani sashe na shi, kuma tuni dai ya ci gaba da aiki bayan dakatarwar wani dan lokaci da ya yi saboda wannan gobarar.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin ya na da kyau kamfanoni da ma kananan masana'antu da daidaikun jama'a su rika bin dokokin kula da kare aukuwar irin wadannan matsalolin domin kauce wa illolin da rashin bin ka'idojin kan iya haifarwa.

Saurari cikaken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG