Mutane Sama Da 603 Suka Rasa Rayukansu A Najeriya Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Mutane Sama Da 603 Suka Rasa Rayukansu A Najeriya Sakamakon Ambaliyar Ruwa

An samu mafi munin ambaliyar ruwa a ‘yan shekarun nan a Najeriya musamman in an kwatanta yawan mutanen da su ka yi asarar rayukansu. Mutuwar mutum 603 a fadin Najeriya ya ninka yawan wadanda su ka rasa rai a bara a sanadiyyar ambaliyar.

ABUJA, NIGERIA - Baya ga samun mutuwar mutane, alkaluman gwamnatin Najeriya sun nuna fiye da mutum miliyan 2.5 su ka jikkata, inda mutum miliyan 1,392 su ka rasa muhallinsu.

Mutane Sama Da 603 Suka Rasa Rayukansu A Najeriya Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Bayan umurnin shugaba Buhari na dankawa ma’aikatar jinkai ton dubu 12 na hatsi don tallafawa wadanda su ka jikkata, ministar ma’aikatar Sadiya Umar Farouk ta ce matakai ne ya dace a dauka a kan lokaci don gujewa fafa gora ranar tafiya.

Ba za a ce ambaliyar ta zo wa jama’ar kasa a bazata ba don hukumar kula da sauyin yanayi NIMET a takaice ta baiyana za a samu ambaliyar, amma rashin daukar matakai daga hukumomi da ma mutanen kan su na rage illar ambaliyar ta hanyar gujewa sassa masu hatsari, rashin share magunan ruwa da yawo ko tuka mota a yayin da a ke tafka ruwan sama sun kara ta’azzara akasin.

Mutane Sama Da 603 Suka Rasa Rayukansu A Najeriya Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Shugaban hukumar ta NIMET Farfesa Mansur Bako Matazu ya ambata dalilan da a kan samu ambaliyar ruwan ciki kuwa da habakar masana’antu da kuma ikon Allah.

Har yanzu dai ba za a ce an rabu da ambaliyar ruwa ba a Najeriya a damunar ta bana don har yanzu akwai sassan da a kan samu ruwan da kuma tumbatsar madatsun ruwa.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Sama Da 603 Suka Rasa Rayukansu A Najeriya Sakamakon Ambaliyar Ruwa.mp3