Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 10 Sun Mutu, 60 Sun Bace Bayan Da Jirgin Ruwa Ya Kife A Jihar Anambra


Ambaliyar Ruwa
Ambaliyar Ruwa

Akalla mutum 10 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kife a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Asabar.

Jirgin mai dauke da mutum 85, ya kife ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye fasinjojin, kamar yadda Thickman Tanimu, kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa

Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Charles Soludo a wata sanarwa da ya fitar ya ce mutum 10 ne suka nutse a ruwa.

Shugaban Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Anambra ya ce an ceto mutum 15 da yammacin ranar Asabar.

Jihar Anambra na tafiyar kimanin awa 6 kudu da jihar Kogi a Najeriya.

Ambaliyar ruwa a jihar Kogi
Ambaliyar ruwa a jihar Kogi

Hukumar ta ce lamarin ya faru ne tsakanin karfe 11 na safe (1000 GMT) zuwa tsakar rana a ranar Juma'a.

Wani mazaunin yankin kuma tsohon shugaban karamar hukumar Afam Ogene ya ce injin kwale-kwalen ne ya gaza, kuma karfin ruwa ta mamaye shi jim kadan da tashinsa.

“Jirgin ruwa ne da aka kera a cikin gida wanda zai iya daukar mutane sama da 100, abin takaici ne da injinsa ya gaza, kuma aka samu turmutsutsu,” inji Ogene.

Anambara na cikin jihohi 29 daga cikin 36 na Najeriya da suka fuskanci ambaliyar ruwa a bana. Ambaliyar ruwan ta kwashe gidaje da amfanin gona da tituna tare da yin illa ga akalla mutane rabin miliyan.

Ogene ya ce ambaliyar ruwa ta lalata babbar hanyar da ta hada al’umomin takwas da sauran kananan hukumomin Ogbaru, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin yin tafiya cikin kwale-kwale.

Manoman sun ce ambaliyar zai kara kaimi ga kudaden abinci a kasar inda miliyoyin mutane suka fada cikin talauci a cikin shekaru biyu da suka gabata.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG