Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Daruruwan jama’a na ci gaba da ficewa daga karamar hukumar Ohaji Egbema ta Jihar Imo, inda ambaliyar ruwa ta lalata sama da gidaje 1000 da gonaki da dama a ‘yan kwanakin da suka wuce.

IMO, NIGERIA - Ambaliyar ruwan dai ta shafi wasu garuruwa 15 ne da ke bangaren Abacheke na karamar hukumar, wani al’amarin da ke wakana bayan wata fashewar da ta lakume rayukan mutum 100 a yankin kimanin wata shiddan da suka gabata.

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Mista Maurice Ogbonna, wani dan asalin karamar hukumar Ohaji Egbema inda barazanar ambaliyar ruwan ke ci gaba da raba mutane da gidajensu, ya yi tsokaci kan halin da ake ciki.

Ya ce, “wadanda suke wuraren da lamarin ya shafa sun bar gidajensu sun nemi mafaka a wasu wurare inda wasu mutane ke taimaka musu. Na ji cewa hukumomi sun ce zasu kawo mana dauki, amma har yanzu bamu ga wani dauki ba. Wasu sun rasa dukiyoyi kuma yanzu suna rayuwa ne daga tallafin wasu mutane suke basu.”

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Ko da yake, shugaban sashen gudanarwa na hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA, Mista Ifeanyi Nnaji ya ce suna kara zurfafa tunani wajen shawo kan matsalar, hukumar dai tana daukar mataki domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

Ya ce, “hukumar ta amince da ba da wasu kayan tallafi don rage tasirin ambaliyar ruwan akan wadanda ta shafa. Al’amarin ya raba mutane da dama da muhallansu. Abin da ake bukata shine samar musu kayan abinci kamarsu shinkafa, wake, garin kwaki, da kuma wasu sinadiran da na iya rage tsananin abin da ya faru.”

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Mista Ifeanyi Nnaji dai ya kara da cewa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta kuduri aniyar ci gaba da yin nazari kan yadda za a dakile ambaliyar ruwa a fadin Najeriya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ta kiyasta gonaki, da amfanin gona, da kuma tasirin ambaliyar ruwan akan manoman yankin, ta kuma fitar da jerin mutanen da al’amarin ya shafa, don tallafa musu wajen maido da abin da suka rasa sakamakon ambaliyar ruwan.

Yanzu bayanai na cewa kimanin mutum 3000 ne sun riga sun fice daga yankin, yayin da ana nan ana jira a ga wace sahihiyar rawa hukumomi zasu taka wajen gaggauta kawo wa al’ummomin da wannan al’amarin ya shafa dauki mai dorewa.

Saurari cikakken rahoto daga Alphonsus Okoroigwe:

Jama’a Na Ci Gaba Da Ficewa Daga Wani Yanki Na Jihar Imo Sakamakon Ambaliyar Ruwa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG